Gwamnan jihar Adamawa Adamu Umaru Fintiri ya gabatar da kasafin kudi na shekarar 2026 da ya hau ra sama da naira biliyan dari biyar ga zauran majalisar dokokin jihar wanda aka yi masa da ci gaba mai dorewa da kuma sabutan ta jihar.
Yace an ware kudi samar da naira biliyan dari biyu ga bangaran gudunarwa, yayi da aka ware wa bangaran aiyukan raya kasa sama da naira biliyan 37 domin ci gaban jihar ta Adamawa.
- Adamawa: Ƴan sandan sun sake ƙaddamar da bincike kan mutanen da aka watsawa acid
- Dakarun Operation Hadin Kai Sun Hallaka ‘Yan Ta’addan Boko Haram 17 A Borno Da Adamawa
- Za Mu Kawar Da APC A Mulki A Zaben 2027 – Atiku Abubakar
Gwamna Adamu Fintiri ya kara da cewa, a kasafin kudin na shekara mai kama wa, gwamnatin jihar tana sa ran kammala aikin hanyar data tashi da Numan zuwa Jalingo domin saukaka harkokin zirga-zirga ta yau da kullum.
Daga bisani majalisar dokokin jihar ta Adamawa ta tabbatar da cewa, zata yi aiki tukuru domin ganin an fara aiki da sabon kasafin kudin akan lokaci domin ci gaban al’ummar jihar ta Adamawa.
