Gwamnatin Kano ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen kawo ƙarshen ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da fataucinsu a faɗin jihar, musamman ganin yadda ƙananan yara ke ƙara faɗawa harkar shaye-shaye.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da sabon ofishin kwamitin karta kwana kan yaƙi da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi, a unguwar Farm Centre.
Gwamnan ya ce sama da kaso 60 cikin 100 na masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da aka gano sun shiga hannun kwamitin, ana ba su kulawa da jinyar da ta dace domin taimaka musu su dawo cikin al’umma.
Gwamnan ya kuma bayyana gamsuwa da nasarorin da kwamitin ya samu tun bayan kafa shi, yana mai cewa kayan aiki da jami’an da ya gani a ofishin sun nuna ƙwarin gwiwar gwamnati wajen magance matsalar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Shugaban Kwamitin Muhuyi Magaji Rimin Gado na gargaɗin matasan Kano, da su guji ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, tare da jaddada cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ganin Kano ta kuɓuta daga matsalar shaye-shaye da fataucin ƙwayoyi.
