Rundunar ’yan sandan jihar Oyo ta kama mutane uku, ciki har da mahaifiyar wata jaririya mai wata ɗaya da kuma mai asibitin da aka haife ta, bisa zargin sayar da jaririyar kan kuɗi Naira miliyan biyu.
Rundunar ta ce ta samu nasarar ceto jaririyar a yankin Ido da ke birnin Ibadan, yayin da take ci gaba da farautar sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Olayinka Ayanlade, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, kakar jaririyar mai suna Mary Amos, mazauniyar yankin Ogunwade da ke Ido, ce ta kai rahoton ɓacewar jaririyar ofishin ’yan sanda a ranar 15 ga Oktoba.
Rundunar ta ce mahaifiyar jaririyar, mai suna Cecilia, ta shaida wa jami’an tsaro cewa mai asibitin mai shekara 40 da wani mutum sun yaudare ta, tare da shirya sayar da jaririyar ga wani mutum mai suna Odunayo.
Binciken farko na ’yan sandan ya nuna cewa an sayar da jaririyar ne kan Naira miliyan biyu, inda ake zargin Cecilia ta karɓi Naira miliyan ɗaya, yayin da sauran mutanen biyu suka karɓi Naira 500,000 kowannensu.
Rundunar ta ce ta ceto jaririyar tare da kama wani mutum mai suna Adeleke, yayin da take ƙoƙarin cafke Folawewo da sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.
Ta kuma jaddada aniyarta ta kare yara da sauran waɗanda ke fuskantar barazanar cin zarafi, tare da kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani zargin safarar yara ga hukumomin tsaro cikin gaggawa.
