Rundunar yansandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata mata mai shekaru 18, Fatima Dalha, bisa zargin soka wa mijinta mai shekaru 30 wuka a ciki, bayan wani rikici kan kuɗi, waya da kayan sawa a Lirr Bajar, ƙaramar hukumar Dass.
Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar jiya Lahadi, inda mijin ya samu rauni kuma aka garzaya da shi asibiti.
Sanarwar ta ce ’yan sanda sun kuma ceto matar daga hannun fusatattun jama’a da suka yi yunƙurin kai mata hari.
A yanzu haka, matar tana tsare, yayin da rundunar ta ce za ta miƙa lamarin ga sashen binciken manyan laifuka na hukumar domin gudanar da cikakken bincike.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi kira ga ma’aurata da su riƙa warware saɓani cikin lumana, tare da gargaɗin jama’a kan ɗaukar doka a hannu.
