Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar tsohon Shugaban gidan Radio Kano, Alhaji Adamu Ibrahim Getso.
Hakan na kunshe ne cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
A cikin sakon, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen dan jarida, kwararren mai gudanarwa kuma jajirtaccen ma’aikacin gwamnati wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bunkasa aikin jarida da wayar da kan jama’a ta hanyar kafafen yada labarai.
Gwamnan ya ce marigayi Getso ya yi fice wajen gaskiya, kwarewa da kuma jajircewa wajen hidimtawa al’umma, lamarin da ya sa ya samu girmamawa daga abokan aiki, jami’an gwamnati da sauran jama’a.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba a madadin gwamnati da al’ummar Kano, yana mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ma’aikatan Radio Kano da ARTV, kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, da daukacin wadanda rasuwar ta shafa.
