Fitaccen jagoran fafutukar kare haƙƙin bil’adama a Amurka, Rabaron Jesse Jackson, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Iyalansa sun sanar da cewa Jackson ya rasu a safiyar Talata, kewaye da ‘yan uwan da abokan arziki.
- Jami’an Amurka da Iran sun fara tattaunawar sulhu a ƙasar Oman
- Kungiyar Amnesty ta nemi a gudanar da bincike kan mutuwar masu zanga-zanga a Adamawa
Jesse Jackson yayi shuhura wajen kare yancin bakaken fata a Amurka musamman a shekarun 1960 bayan haduwarsa da dan gwargwamayar nan Martin Luther King Jr.
Jesse Jackson ya shahara a matsayinsa na jagora a harkokin kare haƙƙin bil’adama, ya ma taba tsayawa takarar shugabancin Amurka a shekarar 1984.
