Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiFadar Shugaban kasa ta ce babu wata rashin jituwa tsakanin Tinubu da...

Fadar Shugaban kasa ta ce babu wata rashin jituwa tsakanin Tinubu da Shettima.

Date:

Fadar shugaban kasa ta karyata zargin da ake na cewa an samu wata baraka tsakanin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ne ya sanar da hakan cikin sanarwar taya Kashim Shettima murnar cika shekaru 58 a duniya.

Nkwocha ya bayyana ikirarin rashin jituwa a tsakanin shugabannin biyu a matsayin karya, inda ya jaddada cewa mataimakin shugaban kasa mutum ne mai biyayya ne ga shugaba Tinubu, sannan yana da alaka mai kyau da sauran manyan jami’an gwamnati.

Ya kara da cewa zargin ya fito ne daga wajen wasu makiya ci gaban Najeriya, da suke son kawo rudani don kawar da hankalin al’umma daga ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke yi a sassa daban daban na kasar.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...