Saurari premier Radio
23.1 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiFadar gwamnatin tarayya ba ta ce komai ba game da makudan kudin...

Fadar gwamnatin tarayya ba ta ce komai ba game da makudan kudin da aka kashe wajen sayo sabon jirgin shugaban kasa.

Date:

Ya zuwa yanzu dai fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja ba ta ce komai game da maƙudan kuɗin da aka kashe wajen sayo sabon jirgin shugaban ƙasa ba, al’amarin da ke ci gaba da yamutsa hazo.

Sai dai wani sabon rahoto ya gano yadda shugaban ƙasar Amurka ke hawa jirgin da aka shafe shekara talatin da hudu ana amfani da shi.

Wannan ya biyo bayan yadda gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabon jirgi kirar Airbus A330, ba tare da bayanin yadda aka samu kuɗin sayen shi, ko kuma sahalewar majalisar Dattawa ba.

An dai fara cece-kuce kan sayen jirgin ne bayan wanda aka saya tun zamanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya fara bayar da matsala a tafiye-tafiyen da aka yi da shi zuwa ƙasashen Saudiyya, da Netherlands, da Afrika ta Kudu.

Wasu bayanan sirri daga fadar shugaban ƙasa sun ce an sayi sabon jirgin ne kawai saboda wanda shugaban ke hawa ya shafe shekaru goma sha tara ana amfani da shi.

Sai dai wancan sabon bincike ya nuna yadda shugaban Amurka ke amfani da jirgin saman da ya shafe shekaru ana amfani da shi, illa dai a kai shi wajen gyara ko sabis, da sauransu.

Fadar shugaban ƙasa, ta sha nanata cewa lalacewar jirgin da shugaban ƙasa ke amfani da shi a nan Nijeriya abun kunya ne, kuma bai dace a ce ana ci gaba da amfani da shi ba, sai dai abun da ya fi ɗaurewa jama’a kai shi ne, yadda aka sayi jirgin, da kuma inda aka samo kuɗin.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...