Saurari premier Radio
29.3 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKamfanin mai na kasa, ya musanta zarge-zargen da ake masa na mayarda...

Kamfanin mai na kasa, ya musanta zarge-zargen da ake masa na mayarda kamfanin OHV da NNPCL.

Date:

Kamfanin mai na gwamnatin tarayya,NNPCL, ya musanta zarge-zargen da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi a cewa sayen kamfanin mai na OHV da NNPCL ya yi wani yunƙuri ne da shugaban ƙasar ke yi na shigar da harkokin kasuwancinsa cikin dukiyar gwamnati.

Cikin wata sanarwa da babban jami’in sadarwa na kamfanin, Olufemi Soneye, ya fitar ya ce Shugaba Tinubu da Wale Tinubu babu ko É—aya daga cikinsu da ke da hannu a sayen kamfanin na OVH.

A cewar NNPCL a lokacin da NNPCL ya sayi OVH a 2022, kamfamin Oando (wanda Wale Tinubu ke da hannayen jari a cikinsa), ya riga ya janye hannayen jarinsa a kamfanin OVH, daga masu kamfanin – Vitol da kuma Helios”, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

Sanarwar ta cigaba da cewa a shekarar 2016 ne kamfanin Oando ya fara janye hannayen jarinsa, inda kamfanonin Vitol da Helios suka zama mamallakan kamfanin É—ungurungum, lamarin da ya sa aka sauya wa kamfanin suna daga Oando zuwa OVH.

A 2019 Oando ya kammala janye hannayen jarinsa daga kamfanin OVH, abin da ya sa kamfanonin Vitol da Helios suka mallaki kashi 50-50 na hannayen jarin kamfanin..

Sanarwar ta ci gaba da cewa bayan NNPCL ya kammala sayen OVH sai duka gidajen man NNPCL da na OVH suka zama rassan kamfanin NNPCL.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...