Rundunar Sojin Najeriya ta kafa kotun soja (court-martial) domin gurfanar da jami’anta 36 da ake zargi da hannu a wani yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
An gudanar da zaman kotun cikin tsauraran matakan tsaro, inda aka hana ‘yan jarida shiga wajen tare da hana amfani da wayoyin hannu yayin shigar da waɗanda ake zargi.
Rahotanni sun bayyana cewa an kai waɗanda ake tuhuma hedikwatar rundunar soji a cikin motar rundunar sojin.
A wani mataki na daban, Gwamnatin Tarayya ta hannun Ofishin Antoni Janar ta gurfanar da wasu mutane shida a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin alaƙa da wannan shiri.
Wadanda ake tuhumar sun haɗa da tsohon Manjo Janar, tsohon Kyaftin na rundunar ruwa, wani jami’in ‘yan sanda mai aiki, da kuma wasu fararen hula.
An gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda 13, inda kotu ta bayar da umarnin tsare su a hannun Hukumar Tsaro ta DSS tare da sanya ranar 27 ga Afrilu domin fara sauraron shari’ar cikin gaggawa.
Rahotanni kuma sun ambaci sunan tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, a cikin binciken, sai dai ana zargin yana gudun hijira.
Lamarin ya fara daukar hankalin jama’a ne bayan soke faretin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga Oktoba 2025. Daga bisani rahotanni suka danganta soke bikin da zargin yunkurin juyin mulki, kodayake rundunar tsaro ta ƙasa ta musanta hakan.
Bayan haka, an tabbatar da cafke wasu jami’an soja da ake zargi da hannu, yayin da wasu kuma suka tsere. A watan Janairu 2026, rundunar tsaro ta ƙasa ta ce bincike ya gano alamun wani shiri na kifar da gwamnati.
Iyalan wasu daga cikin waɗanda ake tsare da su sun fara neman a gudanar da shari’ar a fili domin tabbatar da gaskiya da adalci. Haka kuma, a farkon watan Afrilu, wasu daga cikin iyalan sun gudanar da zanga-zanga a gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa, suna neman a gaggauta shari’ar tare da basu damar ganin ‘yan uwansu.
Masu sharhi na ganin cewa lamarin na nuna muhimmancin bin doka da ƙarfafa tsaro a cikin rundunar soji, musamman a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro daga bangarori daban-daban.
