
Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Hukumar EFCC ta yi nasarar tara dukiyar da ta haura naira biliyan 500 a tsawon shekaru biyu na gwamnatinsu.
Shettima ya bayyana haka ne a yayin wani taron bita da ƙara wa juna sani na alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar Hukumar Shari’a ta Najeriya (NJC) suka shirya a Abuja.
Shettima wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron, ya buƙaci alƙalai da sauran ma’aikata a ɓangaren shari’a da su ƙara ƙaimi tare da yin aiki bisa gaskiya da adalci.
“Ana fara samun matsala ne a ƙasa da zarar masu riƙe da amanar hukunci suka fara tauye haƙƙin mai haƙƙi.
“Gwamnatinmu ba ta tsoma baki a harkokin shari’a, mun ba ɓangaren shari’a da hukumomin yaƙi da cin hanci damar gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba.
“A cikin shekara biyu na wannan gwamnatin, EFCC ta samu nasarar gurfanar da sama da mutum 7,000 a gaban kotu, sannan ta ƙwato dukiyar da ta haura naira biliyan 500,” in ji Shettima.
Mataimakin shugaban ya kuma ƙara da cewa, kuɗaɗen da aka ƙwato ana amfani da su ne a shirye-shiryen tabbatar da walwalar al’umma, ciki har da shirin bayar da bashi ga ɗalibai da sauran manufofin tallafa wa jama’a.