Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci ’yan kasuwar jihar da su yi nazari tare da duba ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar, da kuma shirye-shiryen da kowane ɗan takarar siyasa ya tanada domin inganta rayuwar al’umma, kafin su yanke shawarar wanda za su zaɓa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manya da ƙananan ’yan kasuwar Kano, inda ya ce ya kamata kowane ɗan takarar siyasa, ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake wakilta ba, ya fito gaban al’umma ya bayyana manufofinsa da abubuwan da yake shirin yi wa jama’a idan aka ba shi damar jagoranci.
Gwamnan ya kuma yi kira da kada a mayar da yaƙin neman zaɓe zuwa hanyar zubar da jini, tashin hankali, zagi ko cin mutuncin mutane, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani nau’in yaƙin neman zaɓe da ya ƙunshi cin mutunci ko rashin girmama shugabanni ba.
Da yake jawabi a wajen taron, jagoran ’yan kasuwar Kano, Alhaji Sabi’u Bako, ya bayyana gamsuwar ’yan kasuwar jihar kan yadda gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke tafiyar da harkokin jihar inda yayi tunatar da gwamnatin jihar kan alkawarin bayar da tallafin naira biliyan takwas ga ’yan kasuwar da gobarar kasuwar Singa ta shafa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da sauraron koken ’yan kasuwa tare da ɗaukar matakan da suka dace domin bunƙasa kasuwanci da tattalin arzikin jihar daga farkon watan Oktoba zuwa Disamba masu zuwa.
