Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta naɗa tsohon Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, a matsayin jagoran tawagar masu sa ido kan babban zaɓen Najeriya na 2027.
Sanarwar da ofishin tsohon shugaban ya fitar ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026, ta bayyana cewa ECOWAS za ta tura tawagar mutane 200 domin sanya ido kan yadda za a gudanar da zaɓen.
Tawagar za ta ƙunshi wakilan hukumomin zaɓe, ma’aikatun harkokin waje, ƙungiyoyin fararen hula, ’yan jarida da ƙwararru kan harkokin zaɓe daga ƙasashen yankin.
Ana sa ran tawagar za ta sanya ido kan zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan Majalisar Dokokin Tarayya da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairu, 2027.
Akufo-Addo, wanda ya shugabanci Ghana daga 2017 zuwa 2025, ya taɓa jagorantar tawagar ECOWAS mai sa ido kan zaɓen shugaban ƙasar Benin a watan Afrilun 2026.
