Aminu Abdullahi Ibrahim
Kasar Gabon ta dakatar da amfani da shafukan Facebook da Tiktok sakamakon zargin amfani da su wajen tunzura al’umma da haddasa rikici.
Jean-Claude Mendome mai magana da yawun hukumar dake kula da sadarwa ta kasar ne ya sanar da daukar matakin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar a gidajen talabijin na kasar.
Cikin sanarwar y ace kalaman tsana da na cin zarafi na kawo nakasu ga zaman lafiya da tsaron kasar.
Ya ce akwai karin wasu shafukan na sada zumunta da za a kara sauke su a nan gaba.
Wannan na zuwa ne yayin da al’ummar kasar ke cigaba da caccakar shugaba Brice Oligui Nguema, a kafafen sada zumunta dangane da yajin aikin malamai da kungiyoyin ma’aikata.
