Karamin Ministan Harkokin Masana’antu, Sanata John Owan, ya ce Nijeriya dole ta rage dogaro da shigo da kaya daga waje tare da mayar da jama’a cikin ayyukan samarwa.
Ministan na bayyana haka ne a taron tattalin arziki na RCCG a Legas, inda ya ce nasarar manufar Nigeria-First da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a 2025 za ta dogara da tsayayyen tsari da amfani da sayen kayan gwamnati wajen ƙarfafa masana’antun cikin gida.
A cewarsa yawan jama’a kaɗai ba ya kawo bunƙasar tattalin arziki sai an samar da ayyukan yi.
Ministan ya jaddada cewa idan ba a faɗaɗa masana’antu ba, yawan matasan Nijeriya na iya zama barazana. In da Ya ce haɗa manufofin gwamnati da gyaran tsarin sayayya zai rage shigo da kaya, ya ƙarfafa masana’antu, tare da samar da ayyukan yi masu ɗorewa.
