Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin mulkin soja a Sudan ta yi watsi da tattaunawar zaman lafiya...

Gwamnatin mulkin soja a Sudan ta yi watsi da tattaunawar zaman lafiya da Amurka ta kulla da dakarun RSF a Geneva.

Date:

Shugaban ƙasar Sudan kuma hafsan sojin ƙasar Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya sake yin watsi da tattaunawar zaman lafiyar da Amurka ta ƙulla da za ta fara a Geneva a yau duk da cewa tawagar dakarun RSF ta isa wurin tattaunawar.

A cikin wani jawabin ranar Sojoji Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bayyana cewa zaman lafiya ba zai yiwu ba yayin da RSF ke mamaye garuruwa da ƙauyuka, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da aiyukan soji har sai mayakan sun janye.

Ya jaddada cewa kawo ƙarshen rikicin ya ta’allaka ne kan aiwatar da yarjejeniyar da aka amince da shi a Jeddah daga a Mayun shekarar 2023, wadda ta mayar da hankali kan kare fararen hula da kuma kai agajin jin kai, BBC ta wallafa.

A halin da ake ciki kuma, RSF a cikin wata sanarwa ta X, ta tabbatar da aniyar ta na sassauta wa al’ummar Sudan wahalhalun da ke addabarsu, kana ta bukaci sojojin Sudan da su shiga tattaunawar.

Tawagogin Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Afirka, da Masar sun isa Geneva domin tattaunawar ko da yake babu tabbas ko UAE ta aike da tawaga.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...