Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC kan tsare tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya Honorabul Muhammad Gudaji Kazaure.
Atiku ya bayyyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, a inda ya kuma ce kama Kazaure da kuma tsare shi ya saɓa wa doka.
“EFCC ta sake aikata abin da ta saba na take doka, ta hanyar kamawa da kuma tsare ƴan ƙasa da ba su aikata laifin komai ba”, yana mai bayar da misali da labarin fitaccen ɗan gwagwarmayar nan Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da Verydarkman wanda hukumar ta kama amma ta sake shi bayan matsin lamba daga wajen ƴan ƙasar.
Ya ce ko da akwai abin da mutum ya aikata – to ya kamata a bi hanyar shari’a wajen gurfanar da shi.
Atiku Abubakar ya kara da cewa Hakkin hukumar ne ta fito ta yi wa jama’a bayani kan abin da ya sa ta kama Kazaure, kuma bai kamata su riƙa tsare mutane da sunan yin bincike ba.
Yana mai cewa yan kasa sun zuba ido suna kallo. Kuma tarihi ba zai manta ba.
