Gwamnatin Kano ta ce shirye-shirye sun yi nisa a yunkurin ta na sake gina wasu sabbin madatsu da gidajen rarraba ruwan sha na famfo, domin faɗaɗa ayyukan samar da ruwa ga al’umma, a ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar ƙarancin ruwan sha a faɗin jihar.
Kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa ta Kano, Dr Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai.
Kwamishinan ya kuma yi gargadi da harshe me kaushi kan wadanda suke fasa bututun ruwan da gwamnati ke samarwa al’umma tare da karkatar da shi ya zuwa wasu bukatun su na daban, inda ya ce gwamnati za ta hukunta duk wanda ta kama.
Dr Dahiru ya kuma bayyana cewa yanzu gwamnati ta gyara kusan duka kananan matatun ruwa 19 dake yankunan kananan hukumomin karkara da nufin wadata kauyuka da ruwa mai tsafta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Dahiru na yin alƙawarin gyara dukkan hanyoyin ruwan da suka lalace ko suka daina aiki, tare da ƙara ƙaimi wajen samar da ruwan sha domin sauƙaƙa wa al’umma samun ruwan da suke buƙata.
