Saurari premier Radio
33.3 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWata mata yar shekara 35 ta rasa ranta yayin da gini ya...

Wata mata yar shekara 35 ta rasa ranta yayin da gini ya rufta mata a Kano

Date:

Wani gini mai hawa ɗaya da ya ruguje a unguwar Makwarari a cikin birnin Kano, yayi sandiyar rasa ran wata mata mai suna Balaraba Tijjani yar shekara 35, yayin da yara biyu suka jikkata.

Ginin ya ruguje ne a jiya Juma’a sakamakon mamakon ruwan sama da aka dauki tsawon sa’o’i ana yi a birnin Kano, tin daga daren Alhamis zuwa safiyar jiya Juma’a.

A cewar wani mazaunin unguwar, Abdulnasir, an ceto mahaifiyar da ‘ya’yanta biyu, inda aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano amma daga baya mahaifiyar ta rasu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya ce ginin mai hawa daya ya ruguje ne da misalin karfe 9:30 na safiyar ranar Juma’a.

“Ginin ya murkushe mutane uku, Balaraba Abba mai kimanin shekara 35 da yara biyu, Abdulnasir Jilani mai kimanin shekara 12 da Abdullahi Jilani dan kimanin shekara 9.”

Kakakin ya ce bayan samun labarin, cikin gaggawa suka tura dakarun hukumarsu domin kai daukin gaggawa.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...