Jakadan tarayyar turai EU a Najeriya da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin afirka ECOWAS, Gautier Mignot, ya ce mai yiwuwa Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan mutanen da ke rayuwa cikin talauci a duniya.
Jakadan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taro na bikin ranar kasa da kasa ta kawar da talauci na shekarar 2026, inda ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da abokan hulɗarta su ƙara ƙaimi wajen magance matsalar talauci da ke addabar al’umma.
Mignot ya ce tarayyar turai ta ware kusan yuro miliyan 45 a shekarar 2026 domin tallafin jin ƙai a Najeriya, musamman ga al’ummomin da rikice-rikice, rashin tsaro da sauran matsaloli suka shafa.
Ya bayyana cewa tallafin zai taimaka wajen biyan wasu buƙatu na gaggawa, tare da tallafa wa ayyukan da za su taimaka wa al’ummomi su farfaɗo daga matsalolin da suke fuskanta.
Jakadan ya kuma yi nuni da alkaluman da suka nuna cewa a shekarar 2022, kimanin ’yan Najeriya miliyan 133 na fama da talauci ta fuskoki daban-daban, ciki har da rashin isasshen abinci, matsalolin samun lafiya, ilimi da ingantaccen matsuguni.
Ya jaddada cewa ba za’a iya samun nasarar yaƙi da talauci ba tare da samar da zaman lafiya, tsaro, mutunta haƙƙin bil’adama da kuma hanyoyin da jama’a za su samu damar inganta rayuwarsu ba.
Tarayyar turai ta ce za ta ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya, hukumomin agaji da ƙungiyoyin ci gaba wajen tallafa wa talakawa da sauran masu rauni a cikin al’umma, tare da ƙarfafa shirye-shiryen kariya ta zamantakewa da za su taimaka wajen rage talauci na dogon lokaci.
