Saurari premier Radio
29 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYau ake bikin ranar yan asalin Afirka dake zaune a nahiyoyin duniya

Yau ake bikin ranar yan asalin Afirka dake zaune a nahiyoyin duniya

Date:

Yau 31 ga Augustan 2024 ake bikin ranar yan asalin Afirka dake zaune a nahiyoyin duniya daban daban, domin jinjinawa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban duniya da kuma yaki da wariyar launin fata.

Wannan shekara dai itace ta karshe cikin shekaru 10 da majalisar dinkin duniya ta ware domin gabatar da bikin, daga 2015 zuwa 2024 da aka samu gagarumar nasara wajen kawo canji da kuma sauya tunanin fararen fata masu ta’adar kyamar baki da kallon da suke wa nahiyar Afrika

A jawabinsa kan wannan rana sakatare Janar na majakisar dinkin duniya Antonio Gutteres ya bukaci kasashe da su ja ‘yan asalin Afirka a jika, kuma a dinga damawa dasu a duk harkokin gwamnati domin tabbatar da hadin kai da cigaban kasa da kuma watsi da tsohuwar al’adar nan ta kyamar baki

Sama da mutane miliyan 200 dake da asali daga Afirka ne ke zaune a Amurka baya ga sauran nahiyoyi, kididdiga ta nuna akwai mutane da suka haura biliyan da rabi a yanzu haka a Afrika kuma sune kashi 15 cikin dari na alummar duniya.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...