Sarkin Zurmi a Jihar Zamfara, Bello Suleiman, ya rasu bayan shafe kimanin shekaru biyar yana kan karagar mulki.
Fadar masarautar ta ce Sarkin ya rasu ne da yammacin Litinin a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar.
Bello Suleiman ya zama Sarkin Zurmi a shekarar 2021, bayan ya gaji kawunsa, Abubakar Atiku, wanda gwamnatin jihar ta sauke daga kan karagar mulki a wannan shekarar, kafin daga bisani a hukumance ta tsige shi a watan Afrilun 2022.
An sauke Atiku tare da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, bayan zargin cewa suna da alaƙa da ’yan bindiga tare da tsoma baki a ayyukan jami’an tsaro.
Daga bisani, tsohon Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, ya rasu a wani asibiti a ƙasar Masar.
Marigayi Sarki Bello Suleiman ya mulki Zurmi ne a lokacin da yankin ke fama da matsalar rashin tsaro mai tsanani.
A watan Mayun 2024, ’yan bindiga sun kai hari garin Zurmi, inda suka shiga fadar Sarkin, suka kashe jami’an tsaro uku da ke bakin ƙofar fadar, tare da yin garkuwa da wasu mazauna garin.
