Saurari premier Radio
22.6 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAsusun Tallafa wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya yi kakkausar...

Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya yi kakkausar suka ga ƙasar Somaliya.

Date:

Asusun tallafa wa Ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka ga mahukuntan ƙasar Somaliya kan hukuncin kisa da aka yanke wa wasu matasa huɗu da ake zargi da alaka da ƙungiyar Al-Shabab.

UNICEF ya ce an kashe mutanen huɗu ne a jihar Puntland mai cin gashin kanta a ƙarshen makon da ya gabata saboda laifukan da suka aikata lokacin da suke ƙasa da shekara 18.

Ta ce kotunan soji ba su da wani tsari na musamman na shari’ar yara don haka bai kamata su riƙa yanke wa yara hukunci ba.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata, an kashe mutum 10 ta hanyar harbin bindiga, saboda samunsu da hannu a kisan gilla da tashin bama-bamai a birnin Gaalkayo.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...