Saurari premier Radio
23.1 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniAn nada Bruno Labbadia a matsayin sabon mai horar da tawagar Najeriya...

An nada Bruno Labbadia a matsayin sabon mai horar da tawagar Najeriya ta Super Eagles

Date:

Ahmad Hamisu Gwale

Hukumar kwallon Kafa ta kasa NFF, ta bayyana Bruno Labbadia a matsayin sabon mai horar da tawagar Najeriya ta Super Eagles.

A wata sanarwa da sakataren hukumar, Mohammed Sanusi ya fitar a wannan Talatar, ya ce hukumar ta amince da nada Labbadia a matsayin wanda zai jagoranci Super Eagles.

Dan kasar Jamus, Labbadia zai maye gurbin Finidi Geroge, wanda ya ajiye aiki a watan Yuni.

A yanzu, Labbadia ya kafa tarihin zama mai horar da Super Eagles na 37, kuma dan kasar Jamus na shida da zai jagoranci tawagar bayan Karl-Heinz Marotzke a shekarun 1970 da 1974 da kuma Gottlieb Göller a shekarar 1981.

Sai kuma Manfred Höner a shekarun 1988 da 1989 da Berti Vogts a 2007 zuwa 2008 da kuma na karshe Gernot Rohr daga 2016 zuwa 2021.

A baya, sabon mai horar da Super Eagles din ya jagoranci kungiyoyi irinsu Hertha Berlin, VfB Stuttgart, Bayern Leverkusen, VfL Wolfsburg da kuma Hamburger SV.

An haifi Bruno Labbadia, a ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar 1966 a birnin Darmstadt din kasar Jamus.

Tsohon dan wasa ne da ya taba bugawa kungiyoyin Darmstadt 98 da Hamburger SV da FC Kaiserslautern da Bayern Munich da FC Cologne har ma da Werder Bremen.

Ya kuma yi nasarar lashe gasar Bundesliga da kungiyar Kwallon kafa ta Bayern Munich a matsayin dan wasa a shekarar 1994.

Babban kalubalen dake gaban sabon mai horar da tawagar Najeriya din shi ne, fuskantar wasannin share fagen buga gasar cin kofin nahiyar Afrika da kasar Morocco za ta karbi bakunci.

Inda a watan Satumba mai kamawa, Super Eagles za ta buga wasanni biyu da kasashen Benin da Rwanda domin samun damar buga gasar cin kofin nahiyar Afrika ta shekarar 2025.

Latest stories

Related stories

Sabbin Yan Wasa 12 da Kano Pillars ta dauka

Kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars, wadda ta lashe...