Saurari premier Radio
29 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn kara wa shugabannin riko na kananan hukumomin Kano wa'adin mulki

An kara wa shugabannin riko na kananan hukumomin Kano wa’adin mulki

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amince da karawa shugabannin rikon kananan hukumomin jihar wa’adin watanni biyu akan karagar mulki har zuwa lokacin da za’a samu zababbun shugabanni.

Da yake karanto takardar bukatar karin wa’adin wadda kwamishinan kananan hukumomi kuma mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya aikowa majalisar, shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala, ya ce karin ya zamo wajibi duba da karewar da wa’adinsu ya yi a jiya Lahadi.

Da yake yiwa Premier Radio karin bayani, Hussaini Dala, ya ce karin wa’adin na watanni biyu ya fara ne daga yau Litinin 9 ga watan Satumba, zuwa 9 ga watan Nuwamba mai zuwa ko kuma za su sauka daga mukaman nasu a duk lokacin da aka rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi zababbu.

Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano, Kamal Umar Kurna, ya rawaito mana cewa, Lawan Husaini, dama dokar kasa ta tanadi a nada shugabannin rikon na tsawon watanni uku.

Dokar ta kuma bayar da damar a kara musu watanni uku tare kara musu watanni biyu, wanda a wannan tsakani doka ta wajabta samar da zababbun shugabanni.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...