Kwamitin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucin su na Jihar Kano ya kama wani matashi mai suna Ishaq Lawan Ibrahim, wanda aka fi sani da Malam Keya, bisa zargin ɗaukar nauyin rikicin ƙungiyoyin daba a ƙaramar hukumar Dala.
An kama matashin mai shekaru 27, ɗan asalin unguwar Yalwa a Dala, a birnin Fatakwal na Jihar Ribas, bayan wani samame da jami’an kwamitin suka gudanar bisa bayanan sirri.
A cewar sanarwar kwamitin, ana zargin Malam Keya da jagorantar da kuma ba da kuɗaɗen gudanar da hare-haren ƙungiyoyin daba da suka yi sanadin asarar rayuka da tayar da hankalin mazauna wasu yankunan Dala.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya tsere daga Kano ne bayan jami’an tsaro sun tsaurara matakan yaƙi da ayyukan daba a yankunan Jakara, Madigawa, Yalwa, Sanka, Kul Kul, Dogon Nama, Kukar Bulukiya, Shatsari da Dandalin Turawa.
Jami’an kwamitin ƙarƙashin jagorancin CSP Bashir Gwadabe ne suka bi sawunsa har zuwa Fatakwal, inda suka kama shi tare da dawo da shi Kano domin ci gaba da bincike.
Shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce jami’an tsaro ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamo duk wanda ake zargi da ɗaukar nauyin tashin hankali, ko da kuwa ya tsere zuwa wata jiha.
Ya ƙara da cewa wanda ake zargin yana hannun jami’an tsaro, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamitin ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro ta hanyar bayar da bayanai kan duk wasu ayyukan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu martanin Malam Keya kan zarge-zargen da ake masa ba.
