An fara makokin kwanaki uku a duk faɗin ƙasar Safaniya domin jimamin mutane 40 da suka mutu a haɗarin jirgin ƙasa da ya faru ranar Lahadi da ta gabata a yankin Adamuz, kudancin kasar.
Dai dai lokacin da masu aikin ceto ke ci gaba da yashe ɓaraguzan jiragen biyu da suka yi taho-mu-gama, Firaminista Pedro Sanchez ya sha alwashin gudanar da bincike mai zurfi don gano musabbabin haɗarin.
A cewar Firaministan, wajibi ne a gudanar da bincike mai inganci tare da yin bayani ga jama’a kan dalilan faruwar haɗarin, wanda ya jikkata mutane da dama, baya ga rasuwar waɗanda suka mutu.
Sanchez, wanda ya dakatar da balaguronsa zuwa taron tattalin arziƙi na Davos, ya gaggauta zuwa wurin da haɗarin ya faru tun safiyar Litinin, inda ya ce za a gudanar da makokin kwanaki uku a dukkan sassan ƙasar domin jimama waɗanda abin ya shafa.
Jiragen ƙasan biyu sun yi taho-mu-gama da juna ɗauke da fasinjoji akalla 120, a abin da ake kallon haɗarin jirgin ƙasa mafi muni da Sapaniya ta fuskanta cikin shekaru 80.
