
Gwamnatin Amurka ta bayyana aniyarta na daina bayar da biza ga manyan ‘yan Najeriya da ake samu da laifukan cin hanci da rashawa da kuma karya tsarin dimukuradiyya.
A cikin wani saƙo da ofishin jakadancin Amurka a Abuja ta wallafa a shafinsa na X, kasar ta jaddada cewa ba za a yi sassauci ga duk wani da aka samu da hannu a cikin cin hanci ba, komai matsayinsa ko mukaminsa.
A baya, gwamnatin Amurka ta haramtawa wasu ‘yan siyasar Najeriya biza da ta zarga da yin karen-tsaye da kuma zagon-ƙasa ga tsarin dimokuradiyya.
Sai dai ofishin jakadancin bai bayyana takamaiman lokacin da zai fara aiwatar da wannan mataki ba, amma ya nuna cewa dabarar hana biza wata muhimmiyar hanya ce da Amurka ke amfani da ita wajen karfafa gaskiya da adalci da mutunta doka musamman a ƙasashe da ta ke da dangantaka da su.