
Aminu Abdullahi Ibrahim
Amurka za ta fitar da fasfo ɗauke da hoton Trump
Ma’aikatar Harkokin cikin gida ta Amurka ta ce za ta gabatar da fasfo na musamman wanda zai nuna hoton shugaba Donald Trump.
A cewar Fox News, sabon fasalin fasfo ya kasance na tunawa da murnar cika shekaru 250 da samun ‘yancin kai na ƙasar.
Ana sa ran za a bayar da fasfo ɗin a lokacin bazara a matsayin wani ɓangare na bikin ‘America250’ . Ayyukan da aka tsara sun haɗa da tseren Grand Prix a National Mall a watan Agusta da kuma taron UFC a filin White House South a watan Yuni.
Tommy Pigott, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida ta Amurka, ya ce za a inganta takardun da zane-zane na musamman da kuma ingantattun hotuna, tare da kiyaye abubuwan tsaro na fasfo na Amurka da ake amfani da shi yau da kullun. Wani jami’in ma’aikatar ya ce fasfo din zai kasance ga duk wani dan Amurka da ke neman shiga a lokacin da za a fara amfani da shi.
