
Aminu Abdullahi Ibrahim
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ce idan aka zaɓi tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, hakan ba zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfin samun ƙuri’u ba.
Wike ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya saba gudanarwa kowane wata a Abuja.
Ya ce Amaechi na iya taimakawa yaƙin neman zaɓen Atiku ta fuskar kuɗi, amma a cewarsa, tsohon gwamnan na Ribas ya rasa irin tasirin siyasar da zai iya jawo wa jam’iyyar ƙuri’u.
Ministan ya kuma yi ikirarin cewa ƙarfin ɗan takara ba ya ta’allaka ne kawai kan wanda aka zaɓa a matsayin mataimaki, sai dai kan irin goyon bayan da yake da shi a tsakanin masu zaɓe da kuma yadda jam’iyyar ta samu karɓuwa a faɗin ƙasa.
Kalaman Wike na zuwa ne yayin da ake ci gaba da hasashe da muhawara kan wanda Atiku Abubakar zai zaɓa a matsayin abokin takararsa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
