Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi ga ’yan Najeriya masu fama da wasu cututtuka da su yi taka-tsantsan yayin tafiya ta birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, bayan mutuwar ’yan Najeriya 16 da ke
wucewa ta birnin a shekarar 2026.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana hakan a wata sanarwa da kakakinta, Oluwafemi Adeniyi, ya fitar ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba.
Sanarwar ta ce ana danganta mutuwar mutanen da matsalolin lafiya da ka iya tasowa sakamakon tsayin birnin Addis Ababa daga matakin teku, wanda ya kai kimanin mita 2,355.
Ma’aikatar ta bayyana cewa ƙarancin iskar oxygen da ake samu a wurare masu tsayi na iya jefa masu fama da cututtukan zuciya da na numfashi cikin haɗari.
Saboda haka, gwamnatin ta shawarci matafiya masu irin waɗannan matsalolin lafiya da su nemi shawarar likita kafin tafiya ta Addis Ababa
.
Sai dai ma’aikatar ta jaddada cewa gargadin ba yana nufin an hana ’yan Najeriya tafiya zuwa Habasha ko wucewa ta birnin Addis Ababa ba, illa dai ɗaukar matakan kare lafiyarsu.
