Ƙungiyar AHIP ta buƙaci a ƙara samar da cibiyoyin koyar da sana’o’i da inganta wayar da kan al’umma tun daga tushe, domin rage yawan matasan Kano da ke barin Najeriya zuwa ƙasashen ƙetare ta hanyoyin da ba bisa ƙa’ida ba.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne yayin wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ta shiryawa shugabannin gargajiya da masu ruwa da tsaki a Kano, inda mahalarta taron daga ƙananan hukumomi 9 suka tattauna kan illolin tafiye-tafiyen da ba bisa ƙa’ida ba da kuma hanyoyin da za’a bi wajen samarwa matasa damar samun sana’o’in dogaro da kai.
Jami’ar kula da harkokin mata ta ƙaramar hukumar Gwale, Khadija Imam Abdullahi, ta ce da dama daga cikin matasan da ke yin irin tafiye-tafiye na rasa rayukansu ko fuskantar munanan abubuwa kafin su isa inda suke son zuwa.
Shi ma mai unguwar sarkin Fawa dake ƙaramar hukumar Bunkure, Yusuf Labaran Bunkure, ya ce sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa takawa wajen dakile ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, kasancewar suna da kusanci ga al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito mahalarta taron na buƙatar da a ƙara musu ilimi, kayan aiki da tallafi, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin gano tare da dakile masu jan hankalin matasa zuwa tafiye-tafiye mau haɗari.
