Jam’iyyar ADC ta kafa wani kwamiti mai mambobi guda 50, bayan amincewar Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata David Mark, ne ya amince da kafuwar kwamitin, a wani mataki da ADC ta ce yana daga cikin ƙoƙarinta na samar da ingantaccen shugabanci na gari domin ganin an ciyar da kasar nan gaba ta ko wacce fuska.
A cewar jam’iyyar, kwamitin ya ƙunshi fitattun ’yan Najeriya daga sassa daban-daban, ciki har da tsofaffin masu riƙe da muƙaman gwamnati, malaman jami’o’i, masana a fannin fasaha, shugabannin ƙungiyoyin farar hula da sauran masana.
Wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar ADC na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ta bayyana cewa mambobin kwamitin na da ƙwarewa mai zurfi a fannoni da suka haɗa da shugabanci, tattalin arziki, cigaban al’umma, tsaro da kuma tsarin dimokuraɗiyya.
Sanarwar ta ƙara da cewa Cif John Odigie-Oyegun zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba, yayin da Farfesa Pat Utomi zai kasance mataimakin shugaba, sai kuma Malam Salihu Lukman da aka naɗa a matsayin sakatare.
