Jagoran Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, Khalifa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi, ya yi kira ga hukumomin jami’o’i da gwamnatin tarayya da su tabbatar da adalci ta hanyar ware filaye ko samar da wuraren ibada ga mabiya Ɗarikar Tijjaniyya a jami’o’in ƙasar nan, domin su gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hankali, mutunta juna da zaman lafiya.
Khalifa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana hakan ne yayin zikirin shekara-shekara da aka gudanar a birnin Lafiya na Jihar Nasarawa, inda ya yi bayani, kan matsayar ɗarikar game da buƙatar samar da masallatan Ɗarikar Tijjaniyya a cibiyoyin ilimi.
Ya bayyana cewa manufar wannan buƙata ba ta samo asali daga son rarrabuwar kai ko haifar da wata fitina ba, illa dai tabbatar da adalci da samar da yanayi mai kyau wanda zai bai wa kowa damar gudanar da ibadarsa cikin ‘yanci da kwanciyar hankali kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
A cewarsa, addini yana koyar da haƙuri, hikima da zaman lafiya, kuma mabiya Ɗarikar Tijjaniyya sun daɗe suna tafiya a kan tafarkin mutunci da fahimtar juna domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Sai dai ya bayyana cewa duk da irin haƙurin da suke yi, a wasu lokuta ana fuskantar ƙalubale inda ake dakatar da wasu ayyukansu ko kuma hana su gudanar da wazifa da sauran ibadojin da suke yi na ambaton Allah.
Ya ce manufarsu ita ce samar da yanayi wanda zai ba su damar gudanar da wazifa, mauludi da sauran ayyukan addini cikin walwala ba tare da tsangwama ba, yana mai jaddada cewa kasancewar akwai masallatai daban-daban a al’umma ba yana nufin rarrabuwa ko rabuwar kai ba ne, illa wata hanya ce ta sauƙaƙa ibada da ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna.
Khalifan ya ƙara da cewa idan aka samu wani ƙalubale ko rashin adalci, za su ci gaba da neman mafita cikin hikima, tattaunawa da mutunta hukumomin da abin ya shafa. Idan kuma ba a samu mafita ta wannan hanya ba, za su bi hanyoyin doka da Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya tanada domin kare haƙƙinsu cikin lumana da bin doka.
Ya kuma yi kira mai ƙarfi ga shugabanni da masu ruwa da tsaki a matakai daban-daban da su dawo da hankalinsu wajen tabbatar da adalci da kare haƙƙin jama’a, domin shugabanci amanar al’umma ne, kuma adalci shi ne tubalin zaman lafiya mai ɗorewa. Ya ce babu wata al’umma da za ta samu cikakken ci gaba matuƙar ana tauye wa wasu ‘yancinsu ko hana su gudanar da addininsu yadda suka fahimta cikin tsarin doka da zaman lafiya.
Ya jaddada cewa wajibi ne a bai wa kowane ɗan ƙasa damar gudanar da addininsa cikin ‘yanci a ko’ina, muddin hakan ba ya karya doka ko tauye haƙƙin wani. Ya bayyana cewa idan aka yi wa kowa adalci tare da mutunta juna, za a ƙara samun haɗin kai, fahimtar juna da zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin al’umma.
Ya ƙara da cewa al’umma mai mutunta juna, fahimtar juna da adalci ita ce al’umma mafi albarka, domin duk inda adalci ya zauna, zaman lafiya da ci gaba sukan bunƙasa.
