
Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun yi kira da a sake tsarin yadda ake nada shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC.
Kiraye-kirayen hakan Ya biyo bayan ajiye aiki da Farfesa Mahmood Yakubu yayi bayan cikar wa’adinsa na biyu.
Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Najeriya ne ya yi kiran samar da wani kwamitin da zai jagoranci nada sabon shugaban hukumar da kuma kwamishinoninta.
A ranar Talata ne Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙaminsa na shugaban hukumar zaɓen Najeriya tare da miƙa ragamar jagorancin Inec ga May Agbamuche kafin naɗa sabon shugaba.
Kundin tsarin mulki ya ba shugaban kasa damar zaɓen shugaban hukumar bayan tuntubar majalisar ƙasa da ta ƙunshi tsoffin shugabanni da gwamnoni da shugabanannin majalisun tarayya.
” Idan har ana son tabbatar da hukumar zaɓen a matsayin mai ƴanci kuma mai zaman kanta da kuma tabbatar da tsabtar tsarin zaɓe, akwai buƙatar sake tsarin zaɓen shugabannin hukumar.
“Akwai buƙatar samar da kwamiti na musamman mai zaman kansa wanda zai ƙunshi wakilan jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hula da kuma kwamitin majalisun tarayya wanda za a ɗora wa alhakin zaɓen sabon shugaban hukumar”. In ji su.
Ana sa ran a wannan mako Shugaba Tinubu zai bayyana wanda zai zama sabon shugaban hukumar, yayin da ya tanadi jerin sunayen da yake son gabatarwa majalisar a gobe Alhamis.