Majalisar zartaswar gwamnatin Kano ta amince da ware kashi 64 cikin 100 na daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027, wanda ya kai naira tiriliyan ɗaya da biliyan 107, domin gudanar da ayyukan raya ƙasa, yayin da aka ware kashi 36 cikin 100 domin ayyukan yau da kullum.
Amincewar ta biyo bayan zaman da majalisar zartarwar ta gudanar a daren Lahadi zuwa wayewar garin yau Litinin wanda Gwamna Abba ya jagoranta, inda aka sake yin nazari kan daftarin kasafin kuɗin kafin gwamnan ya gabatarwa da majalisar dokokin jihar shi domin neman amincewar su.
Da yake yiwa Premier radio ƙarin bayani, kwamishinan yaɗa labaran Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce tsarin kasafin ya nuna an fi mayar da hankali ne kan ayyukan raya ƙasa domin inganta rayuwar al’ummar jihar.
A nasa ɓangaren, kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare Musa Suleiman Shanono, ya ce jimillar kudirin kasafin ya zarce naira tiriliyan ɗaya da biliyan 107, inda ake hasashen samun naira biliyan 142 daga kuɗaɗen shiga na cikin gida, yayin da ake sa ran gwamnatin tarayya za ta samar da naira biliyan 529.
Wakilinmu a gidan gwamnatin Kano, Kamal Umar Kurna, ya ruwaito cewa majalisar ta kuma baiwa sababbin kwamishinoni 8 da Gwamna Abba ya rantsar a makon da ya gabata, wa’adin sa’o’i 24 domin yin nazarin abubuwan da aka tsarawa ma’aikatunsu tare da gabatar da shawarwarin da za su taimaka wajen inganta ayyukansu.
