Aljeriya da Najeriya za su buga zagayen ƙwata fainals ranar Asabar din nan a Marrakech a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Morocco.
Aljeriya mai Afcon biyu da ta ɗauka a 1990 da kuma 2019, ta kai zagaye na biyu a wasannin da Morocco ke gudanarwa da lashe dukkan karawar rukuni na biyar da haɗa maki tara.
Ta fara wasan farko da cin Sudan 3-0 da doke Burkina Faso 1-0 da yin nasara 3-1 a kan Equatorial Guinea.
Daga nan ta fitar da Jamhuriyar Congo da cin 1-0 a zagaye na biyu a minti na 119 ta hannun Boulbina daf da za a tashi a karin lokaci.
- Morocco Ta Yi Nasara a Wasan Bude Gasar AFCON 2025
- Hakimi ya zama gwarzon kwallon kafa na Afrika na 2025
- Kano ta doke Kaduna a gasar Kwallon UBEC na ‘yan kasa da shekaru 13
Ita kuwa Najeriya rukuni na uku ta ja ragama da lashe dukkan wasa uku da maki tara.
Ta fara da nasara a kan Tanzaniya 2-1 da cin Tunisia 3-2 da doke Uganda 3-1, sannan ta yi waje da Mozambique 4-0 a wasan zagaye na biyu.
Da zarar an tashi daga wannan wasan, duk wadda ta yi nasara za ta kara da Morocco ranar Laraba a wasan daf da karshe a Rabat.
Morocco ta kai zagayen daf da karshe ranar Juma’a bayan da ta doke Kamaru 2-0.
Itama Senegal ta kai daf da karshe, bayan cin Mali 1-0 a ranar ta Juma’a, wadda za ta fuskanci duk wadda ta yi nasara tsakanin wasan Masar da Ivory Coast da za a yi ranar Asabar.
