Saurari premier Radio
33.3 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ba ta kara harajin VAT ba - Wale Edun

Gwamnatin tarayya ba ta kara harajin VAT ba – Wale Edun

Date:

Ministan tattalin arziki, Wale Edun, ya karyata rahotannin da ke cewa an kara harajin VAT zuwa kashi 10% daga kashi 7.5.

Ministan, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, ya tabbatar da cewa harajin na VAT yana nan kashi 7.5%. kamar yadda yake kunshe a cikin dokokin haraji.

Ya ce don haka gwamnatin tarayya ko wata hukumar bata da damar da za ta yi wani abu da ya saba dokin harajin.

Ministan ya kara da cewa jita-jitar da wasu kafafen yada labarai ke yadawa kan batun harajin VAT, suna nuna cewa gwamnati na shirin kawo wa yan Najeriya wahala, wanda kuma ba haka bane.

Ya kara da cewa a kokarin da gwamnatin ke yi na saukakawa yan kasa da yan kasuwa, ko a kwanakin nan sai da gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin dakatar da harajin shigo da kayayyaki daga kasashen waje da suka hada da shinkafa, alkama, wake da sauran kayan abinci.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...