Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa ’yan Najeriya ba za su iya gudanar da bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai cikin farin ciki na gaskiya ba, matuƙar miliyoyin al’umma na ci gaba da fama da talauci, yunwa, rashin aikin yi da matsalar tsaro.
Sowore ya bayyana hakan ne a cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, yayin da ƙasar ke bikin zagayowar ranar samun ’yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, 2026.
Ya ce duk da cewa Najeriya ta samu ’yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekarar 1960, har yanzu al’umma da dama ba su amfana da muhimman abubuwan da ’yancin kai ya kamata ya samar ba, kamar walwala, mutunci, adalci da wadata.
Sowore ya kuma soki halin da ilimi, kiwon lafiya da samar da wutar lantarki ke ciki, yana mai cewa ma’aikata da dama na karɓar albashin da ba ya wadatar da iyalansu, yayin da manoma ke fuskantar barazanar rashin tsaro.
Ya zargi gwamnatocin da suka shuɗe da na yanzu da gazawa wajen amfani da arzikin ƙasa yadda ya kamata, yana mai cewa ’yan Najeriya sun cancanci samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya da ilimi, wutar lantarki mai ɗorewa da kuma damar gudanar da sana’o’insu cikin aminci.
Sowore ya jaddada cewa aikin da ke gaban al’umma bai tsaya ga bikin ’yancin kai da aka samu a 1960 ba, illa gina Najeriya mai ’yanci daga cin hanci da rashawa, danniya, talauci, rashin adalci da rarrabuwar kawuna.
Ya ce wajibi ne a gina ƙasar da za ta yi aiki domin amfanin kowane ɗan ƙasa, ba wai wasu tsirarun masu gata kaɗai ba.
