Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Dakta Mansur Mukhatar a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar bankin masana’antu na kasa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar a Litinin din nan, ta ce shugaban ya amince da nadin Dakta Mansur da karin mutane 12.
Dakta Mansur Muhtar wanda shi ne Sarkin Ban Kano, kuma Hakimin Dambatta ya zama sabon shugaban hukumar gudanarwar ne bayan amincewar shugaba Bola Tinubu.
A baya ya rike mukamin ministan kudi da kasafi daga shekarun 2008 zuwa 2010, kuma shi ne mataimakin shugaban bankin ci gaban musulunci.