Akanta Janar na Ƙasa, Shamseldeen Ogunjimi, zai gurfana a gaban Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai a yau Litinin domin amsa tambayoyi kan yadda aka warewa wata hukumar bogi fiye da Naira biliyan 1 da miliyan dari 3 da 20 a cikin Kasafin Kuɗin 2026.
Kwamitin, wanda ɗan majalisar daka Jihar Filato, Yusuf Gagdi, ke jagoranta, na gudanar da bincike kan yadda aka kafa Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), wata hukuma da Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta san da wanzuwarta ba.
Ana sa ran zaman zai mayar da hankali kan yadda aka sanya kuɗaɗen hukumar cikin kasafin kuɗi da kuma gano waɗanda ke da hannu a lamarin.
