Wasu rahotanni daga Jihar Neja sun bayyana cewa an kai hari da abubuwan fashewa kan turakun wutar lantarki guda biyu da ke haɗa tashar samar da wutar lantarki ta Kainji da Jebba.
Rahoton Zagazola Makama, wanda ke bibiyar al’amuran tsaro, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na rana a ranar Talata, 17 ga Nuwamban 2026, tsakanin garin Kanti a ƙaramar hukumar Mashegu da Kanya a ƙaramar hukumar Mokwa.
Majiyoyin tsaro da rahoton ya ambata sun danganta harin da wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, sai dai ba a samu tabbacin hakan daga hukumomin tsaro ba.
Rahoton ya ce fashewar ta haddasa fargaba tsakanin mazauna yankunan da ke kusa, amma babu wanda aka ruwaito ya rasa ransa.
Ana zargin cewa maharan sun yi niyyar lalata muhimman kayayyakin jigilar wutar lantarki, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da sanya ido a yankin.
Har yanzu ba a tabbatar da girman lalacewar turakun ko tasirin lamarin kan samar da wutar lantarki ba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan hare-hare da lalata kayayyakin wutar lantarki a sassa daban-daban na Naje
