
Gwamna Abba Kabir Yusuf yana jawabi a yayin taron
Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce, babu gudu ba ja da baya kuma babu tsoron magauta, kuma babu damuwa duk abin da za su ce su fada in Allah ya yadda za su cigaba da abi nda suke yi na aikin alheri.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da rabawa tsoffin kansilolin kudaden su a gidan gwamnati ranar Laraba a fadar gwamnatin Kano yayin bikin biyan tsaffin Kansiloli hakkinsu da gwamnatin baya ta hana.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya ce, kudaden da aka biya tsoffin kansiloli hakkin su ne da yakamata a ce tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta biya su amma ta danne musu hakki.
Abba Kabir Yusuf ya ce, jajircewa da kokari da tsoffin kansilolin na da, da na yanzu su ka yi shi ya sa gwamnatinsa ta yanke hukuncin biyansu harkokin su.
Gwamnati ba ta nuna banbanci dangane da bangaren da kansilolin suka fito ba wajen biyansu. Kuma saboda yawan kudin fiye da biliyan 16 da gwamnatin baya ta hana su, gwamnatinsa ta kasa kudin gida uku.
“Kaso na farko gida na tsofaffin kansiloli ne wadanda suka yi aiki daga 2014 zuwa 2017 su 903 inda aka basu naira biliyan 1, 805, 3,823, 20
“Ka shi na biyu tsoffin kansiloli ne daga 2018 zuwa 2020 su dubu 1,198, wanda a farkon watan Yuni zuwa Yuli zasu karbi kudi naira biliyan 5,604,205,998,70.
“Rukuni na uku da suka yi mulki daga 2021 zuwa 2024 su 1,371 daga watan Agusta zuwa Nuwamba zasu karbi biliyan 8,258,424,823,20.
Ko a ranar Larabar nan mun biya kansiloli masu ci kudin alawus din su na gida da kayan alatu naira biliyan 1,273,762,846,92″ In ji gwamnan.

Abba Kabir Yusuf ya yi kira da su yi amfani da kudin yadda yakamata don inganta sana’a da kyautatawa iyali da sauran al’umma.
Haka zalika yayi kira ga tsoffin kansilolin su hada kai da gwamnatin Kano domin dawo da martabatar jihar Kano.
Ya ce tabbatar da kiwon lafiya, ilimi, da kyautatawa al’umma wajen sama musu sana’o’i da basu jari shine abinda gwamnati ta sa gaba.