Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Bankin Duniya da kada ya amince da sabon bashin dala miliyan 500 da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke neman karɓa, yana mai zargin gwamnatin da ƙoƙarin ɗora wa gwamnati mai zuwa nauyin biyan sabon bashi gab da sauka daga mulki.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce bai kamata gwamnatin da ke shirin barin mulki ta ɗauki sabon bashi wanda zai zama nauyi ga magajinta da kuma ’yan Najeriya ba.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da jinginar da makomar ƙasar, tare da kira ga Bankin Duniya da ya ƙi amincewa da buƙatar bashin.
Ya kuma yi ikirarin cewa an tsara gabatar da buƙatar bashin dala miliyan 500 domin tantancewa a ranar 25 ga Mayun 2027, kwanaki huɗu kacal kafin rantsar da sabon shugaban ƙasa.
Atiku ya ce: “Shugaba Tinubu ba shi da wani dalilin ɗora wa ƙasar sabon bashi a daidai lokacin da yake shirin barin ofis.
