Saurari premier Radio
25.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKOTU TA UMARCI A RUFE ASUSUN BANKI NA WASU MUTANE 32 DA...

KOTU TA UMARCI A RUFE ASUSUN BANKI NA WASU MUTANE 32 DA AKE ZARGIN SUNA DA ALAKA DA ZANGA-ZANGAR ADAWA DA TSADAR RAYUWA TA KWANAKI 10 DA AKA GUDANAR A FADIN NIGERA

Date:

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta rufe  asusun banki na wasu mutane 32 da ake zargin suna da alaka da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta kwanaki 10 da aka shirya a fadin kasar.

Kotun ta umarci a cigaba da rufe asusun bankunan wadanda ake zargin sun dauki nauyin tashe-tashen hankulan da aka samu yayin zanga-zangar a wasu jihohin har zuwa lokacin da za a kammala gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Mai shari’a Emeka Nwite, a hukuncin da ya yanke kan karar da lauyan Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Mohammed ya gabatar, ya kuma umurci bankunan da su dakatar masu asusun ajiyar ko duk wani mutum da ke yin kasuwanci a asusun ajiyar.

Mai shari’a Nwite, ya kuma umurci bankunan da su tuntubi rundunar ‘yan sandan kasa da zarar an dakatar da masu asusun.

Kotun ta kuma umurci bankunan da su fitar da cikakkun bayanai na shige da fitan kudi a asusun, hadi da dakatar da fitar kudi daga asusun da kuma dakatar da katin cirar kudi na ATM na asusun.

Lauyan Yan sandan ya bayyanawa kotun cewa ana amfani da asusun ne wajen daukar nauyin aikata laifuffukan da ba da tallafin ta’addanci, cin amanar kasa, cin zarafi ta yanar gizo da kuma yin amfani da yanar gizo ba bisa ka’ida ba.

Ya kara da cewa, wadanda ake zargin na da hannu wajen karbar tutar wata kasa ta bazawa alumma suka dinga dagawa yayin zanga zangar wanda cin amanar kasa ne kararara.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...