Hukumar lafiya ta duniya WHO tace samar da motocin daukar marasa lafiya guda 484 ga cibiyoyin kula da lafiya matakin farko a jihar kano zai taimaka wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.
Wakilin WHO Dr Mayana ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da motocin, inda yace motocin za su saukaka jigilar marasa lafiya daga kananan asibitoci zuwa manyan asibitoci cikin gaggawa, musamman a yankunan da ke da matsalar sufuri.
Ya ce samun damar kai marasa lafiya asibiti a kan lokaci na da matukar muhimmanci wajen ceton rayuka, musamman masu bukatar kulawa cikin gaggawa.
Daga bisani WHO ta yaba wa gwamnatin Kano bisa wannan mataki, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da hadin gwiwa da jihar wajen inganta harkokin kiwon lafiya.
