Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon Shugaban hukumar bunƙasa noma da raya karkara ta Kano, KNARDA, Malam Sani Shawai, wanda ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.
Gwamnan ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ciki har da ‘yan jarida Ibrahim Sani Shawai, da Kamaluddeen Sani Shawai, babban sakataren yaɗa labaran kakakin majalisar dokokin kano; da Muhammad Bello Sani Shawai na DW Radio.
Malam Sani Shawai, wanda ya taɓa aiki a matsayin malami da jami’in ilimi a tsohuwar jihar Kano, ya kwashe shekaru yana hidima a fannin ilimi da aikin gwamnati, tare da barin mata uku, ’ya’ya da jikoki masu yawa.
Gwamna Yusuf ya bayyana marigayin a matsayin dattijo mai daraja, wanda rayuwarsa ta kasance cike da hidima ga al’umma, kishin ilimi da sadaukarwa wajen kula da iyalansa da ci gaban al’ummarsa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba na roƙar Allah ya bai wa iyalansa, ’yan uwa da abokan aikinsa da sauran waɗanda rasuwar ta shafa juriyar jure rashin sa da roƙa masa aljanna maɗaukakiya a wajen Allah.
