Shugaban kasa Bola Tinubu ya mayar da martani game da zargin da ƴan adawar ƙasar nan ke wa jam’iyya mai mulki na cewa tana son mayar da ƙasar kan tsarin jam’iyya ɗaya.
Tinubu ya mayar da martanin ne a cikin jawabinsa na ranar dimokurɗiyyar ƙasar nan, yau Alhamis 12 ga watan Yunin 2025 a zauren majalisar dokokin ƙasa.
Sai dai shugaban ya ce wannan ba zai hana jam’iyyar APC yin maraba da duk wanda ke son shiga cikinta ba.
A baya-bayan nan jam’iyyar APC ta karɓi wasu daga cikin gwamnoni da sanatoci da kuma ƴan majalisar dokokin tarayya da suka sauya sheƙa zuwa cikinta daga jam’iyyun adawa.
Sai dai jam’iyyun adawar sun zargi APC da kuma shugaba Tinubu da shafa wa ƴan siyasar zuma a baki domin jan hankalinsu su koma cikin jam’iyyar mai mulki.
Tuni dai fagen siyasar kasar nan ya ɗauki zafi duk kuwa da cewa a watan da ya gabata ne gwamnati mai ci ta ci rabin wa’adin shugabancinta na shekara huɗu.
