Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da rijiyoyin burtsatse guda 166 masu amfani da hasken rana a sassa daban-daban na jihar domin magance matsalar karancin ruwa da kuma inganta samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.
Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar, Dr Dahiru Hashim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce shirin na daga cikin matakan gaggawa da gwamnatin jihar ke dauka domin rage matsin karancin ruwa a yankunan da abin ya shafa.
Ya ce ana sa ran rijiyoyin za su samar da kimanin lita miliyan 4.15 na ruwa a kullum, tare da amfani ga kusan mutane 830,000 a fadin jihar.
A cewarsa, kowace rijiyar daga cikin guda 166 za ta rika samar da kimanin lita 25,000 na ruwa a rana.
Hashim ya bayyana cewa wannan shine mataki na farko na aikin, yana mai cewa Gwamnatin jihar za ta ci gaba da amincewa da karin rijiyoyi domin fadada aikin zuwa wasu yankunan jihar.
Ya kuma bayyana cewa an fara aikin gyaran cibiyoyin tace ruwa na Tamburawa da Challawa bayan Gwamnatin jihar ta amince tare da bayar da kwangilar ayyukan.
