Saurari premier Radio
24 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMutane 16 ne suka rasu, 3,986 suka rasa matsugunansu yayin da fiye...

Mutane 16 ne suka rasu, 3,986 suka rasa matsugunansu yayin da fiye da hekta 2,744 na gonaki suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa.

Date:

Mutane 16 ne suka rasu, 3,986 suka rasa matsugunansu yayin da fiye da hekta 2,744 na gonaki suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye kauyuka a fadin kananan hukumomi 10 na jihar Jigawa.

Sakataren zartarwa na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, Dr. Haruna Mariga ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayar da cikakken bayani game da iftila’in ambaliyar ruwan da ta mamaye kananan hukumomi 10 na jihar.

Mariga ya bayyana cewa, duk da cewa damina ba ta kai kololuwarta ba, amma asarar da aka samu ya zuwa yanzu na da matukar tayar da hankali, saboda fargabar lamarin na iya ta’azzara ganin yadda ruwan ke ci gaba da karuwa.

Shugaban SEMA ya bayyana cewa, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA sun fara raba kayan agaji da suka hada da kayan abinci ga wadanda lamarin ya shafa.

 

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...